Rundunar sojin ruwan Najeriya, a jiya Asabar ta ce, bangaren rundunar na Operation Dakata Da Barawo, sun yi nasarar cafke danyen mai da ya kai Naira miliyan 613 da aka sace tare kuma da tacewa ba bisa ka’ida ba, Automotive Gas Oil a turance, wanda aka fi sani da dizal daga hannun barayin mai da sauran masu aikata laifuka a yankin Neja-Delta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojojin ruwan Najeriya, Commodore Kayode Ayo-Vaughan, ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, farmakin manuniya ce ta kudurin da sojojin ruwan Najeriya suka dauka na tabbatar da cewa ba za a iya jure ma satar danyen mai ba da hada-hadar tukwanen gas ba bisa ka’ida ba, da kuma aikata sauran laifukan da suka shafi tattalin arziki a yankin ba.
Ayo-Vaughan, ya gargadi masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da masu daukar nauyin su, da su kauracewa ayyukan rashin kishin kasa da aikata laifuka a yankin,inda ya ce an kama kayayyaki na makudan kudade, cikin makonni biyu.
“Wannan kamawa da kwacewa daga rundunar ta ayyuakan dakatar da barawo(OPDDB) da ake ci gaba da yi, sun dakile barayin mai da masu aikata laifuka kusan Naira miliyan 200 da dala 700,000 a cikin makonni 2. Hakan na nuni ne da kudurin rundunar sojojin ruwan Najeriya na tabbatar da cewa ba za a iya jure wa ayyukan satar mai da cin hanci da rashawa da kuma laifukan karya tattalin arziki masu alaka da yankin tekun kasar da musamman yankin Kudancin kasar ba.” in ji shi.
Da yake ba da cikakken bayani game da kame-kamen da aka yi a makonnin da ake nazari, Ayo-Vaughan, ya ce, “A ranar 5 ga Afrilu 2022, Jirgin ruwan Sojojin Ruwa na Najeriya PATHFINDER a Fatakwal, ya kama manyan kwale-kwalen katako guda tara.
Bugu da ƙari, an gano wuraren da ake tace man ba bisa ka’ida ba tare da tukwane, tankuna da tafkunan ruwa a Ketoru Creek. Rundunar ta kuma kama wasu kwale-kwale BOATS DOROH 1 da DOROH 2 da suke rakiya ba bisa ka’ida ba a yankin Bonny martime ba tare da ingantaccen izini ba.