Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi  ya koma jam’iyyar PDP

Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Abubakar Sulaiman, a jiya Asabar, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC, zuwa jam’iyyar PDP.

Shugaban majalisar wanda shi ne shugaban taron shugabannin majalisar dokokin jihar, ya bayyana haka a lokacin buda baki na watan Ramadan da gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Mohammad ya shirya ma jigajigan jam’iyyar PDP daga Ningi da Toro da Warji da Dass a Gidan Gwamnati.

Shugaban majalisar ya ce, ya yanke shawarar sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne saboda la’akari da kyakkyawan salon jagoranci na Gwamna Mohammad da kuma jajircewarsa na kawo sauyi a jihar.

A cewarsa, ci gaban Gwamna Mohammed ya sa shi ya koma jam’iyya mai mulki a jihar.

Daga nan Sulaiman ya yabawa gwamnan kan abin da ya kira iyawarsa na tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa na gwamnati da majalisar dokokin jihar.

A cewar shugaban majalisar, gwamnan ya samu nasarar hakan ne duk da rarrabuwar kawuna a jam’iyyar, inda ya ce dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu ta ba da damar tsarawa da aiwatar da tsare-tsare a jihar.

A martaninsa kan lamarin, Gwamna Mohammad ya bayyana cewa, babban abin alfahari ne da shugaban majalisar ya yi masa.

Gwamnan ya ce, gwamnatinsa ta zabi fara gudanar da ayyukan raya kasa a fadin jihar da nufin samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar, maimakon inganta cin hanci da rashawa ta hanyar raba dukiyar gwamnati a tsakanin wasu tsirarun mutane.

Daga nan sai ya nemi goyon baya da hadin kai ga gwamnatinsa, da nufin tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a jihar Bauchi.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hamza Koshe Akuyam, ya yi maraba da shugaban majalisar zuwa jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa Sulaiman na daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa da suka koma PDP. A cewarsa, tare da aiki da iyawar jam’iyyar PDP, za ta samu nasara a zaben 2023 a jihar da ma kasa baki daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *