Masu hikima da iya salon magana sun ce “Tafiya da gwani mai dadi”.
Kuma liman shine sallah, madugu shine tafiya, jagoranci sahihi shi ke ishara ga sahihiya kuma ingantacciyar tafiya.
A takaice, dukkan lamarin da ake so a ga yayi aqiba mai kyau, ko na kasuwanci,ko zamantakewa ko addini ko siyasa, samun nasara ko akasin haka, ya ta’allakane ga wadanda aka baiwa jagorancin wannan lamari.
Bisa wadannan misalai da suka gabata ne, shahararriyar jam’iyyar nan mai farin jini watau S.D.P a Jihar Katsina ta yima kanta kiyamullaili, tayi nika da tankade da rauraya a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu,2022, ta zabi dattijo, haziki, jajirtacce, kuma dan kishin kasa, Alh Bello Adamu Safana a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha.
Tun daga ranar da labari ya bayyana cewa, Bello Safana shi zai jagoranci tafiyar wannan jam’iyya a Jihar Katsina, masana masu hangen nesa, da sanin abinda jiya tayi, da yau da kuma hasashen abinda gobe zata haifa, sukayi nisa wajen kallon kyawon da wannan tafiya za tayi, lura da sanin kwarewa da kima da mutunci da amanar Wmwanda aka zaba yayi wannan jagoranci.
A bangare daya kuma illahirin jam’iyyun siyaya dake fadin jiha, ciki ya duri ruwa, domin suna kallon yan taurarinsu dake kyalli rana zata disashesu, ta hasken SDP karkashin Alh Bello Adamu Safana.
Masu zance na fadin “Shi dai zinari zinarine koda ba’a kerashiba.” Ma’ana yana nan da kima da darajarshi. Duk da shahara da suna da Alh Bello Safana yayi ba zai hana mu kara bayyana wa al’umma bayani a kansa ba.
An haifi Bello Adamu Safana a ranar 30 ga Mayu, 1959. Kuma yayi digrinsa na farko akan nazarin halittar kasa(Geography) daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria, yayi digiri na biyu a Jami’ar Bayero (BUK( da je Kano akan harkokin cinikayya, sannan yayi babbar diploma akan sha’ani gudanar da shugabanci,(PGDM) a BUK; haka kuma ya samu fita a kasar Birtaniya, inda yayi wata babbar diploma akan kididdiga da al’kalumma da cigaba(PGDDS,IDS) a jami’ar Suxxex,Falmer Brighton.
Haka kuma Alh Safana ya samu halarta taruka na karawa juna sani(seminars/workshops) a ciki da wajen kasar nan.
Masu magana na cewa”ilimi daban, aiki daban”.Sabon shugaban Jam’iyyar SDP a Jihar Katsina, ya yi ayyuka daban-daban a shekaru masu yawa, kuma yana da cikakken tarihi na kwarewa, da rikon amana, da gaskiya da jajircewa akan ayyukan da ya aiwatar.
Yayi aiki Sashen Kasafin Kudi da Tsare-tsare a Ma’aikatar Kudi ta jihar Kaduna dama Jihar Katsina daga 1982-1994. Daganan kuma yayi aiki da Hukumar IFAD daga 1994 -2000.
Hakanan Safana ya yi aiki da Hukumar Kula da Cigaban Ayyukan Noma da Cigaban Al’umma (Katsina State Agriculture and Community Development Project) a matsayin darektan tsare-tsare da kula da ayyuka.
Daga nan kuma ya zama daraktan Tsare-tsare da kula da ayyuka na hukumar KTARDA tun daga 2001-2013. Har wa yau, Alh Bello yayi aiki matsayin kwararre na tuntuba a shirin DFID a Jihar Katsina daga 2013-2016.
Wannan fa shine Sabon shugaban jam’iyyar SDP a Hihar Katsina, mutumen kirki, dattijo, wanda ya sadaukar da akasarin rayuwarsa akan ayyukan cigaban al’ummar jiharsa ta Katsina.
Kuma ba sbu bane boyayye cewa dukkan inda Bello Adamu yayi aiki ya bar kyakkyawan tarihi da abun koyi ga yan’ baya; sabanin shugabannin wasu jam’iyyun dake ikirarin kawo cigaban jihar, amma mazaunan su dankare suke da najasar cin amana, zamba cikin aminci da sama da fadi da dukiyar al’umma.
A saboda haka shidai ido ko ba ma’auni bane, ya san kima.
Al’ummar Jihar Katsina ku yi jerin gwano ko farin-dango tare da goyawa Alh Bello Adamu Safana baya ta hanyar shiga wannan jam’iyyar da ya ke jagoranta domin samun canji na gari kuma maidorewa, da ingantacciyar rayuwa da cigaban tattalin arziki, ta hanyar inganta tsaro, da noma da kiwo, da ma sauran bangarorin na rayuwar yau da kullum.
Alh Bello Adamu Safana, “mun bi, mun yi mubaya’a, kafarka kafarmu”.!!!