Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Mali da ta daina hada kai da dakarun Rasha.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Kanar Assimi Goïta a birnin Bamako a ranar Laraba. Ministar ta ce, laifukan da ake aikatawa a Mali suna da salon irin wanda sojojin Rasha ke amfani da shi a Syria da Ukraine. “Na bayyana a fili cewa wannan damuwar, ta fi dukkan ayyukan kungiyar tarayyar turai. Ba za mu iya ci gaba da yin aiki tare ba, muddin ba a yi wata iyaka da sojojin Rasha ba, kuma ba haka lamarin yake ba a halin yanzu. Dalilin da ya sa ba za mu iya ci gaba da aiki a nan Mali ba kamar yadda yake. “in ji ta.
Wasu sojojin Jamus 300 ne ke cikin aikin horarwa da kungiyar Tarayyar Turai ke yi a Mali.
Yayin da Baerbock ta bayyana fargabar aikata laifuka kan fararen hula na kasar Mali, ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop ya bukaci abokan huldar kasashen waje, su mutunta zabin Mali, yana mai karyata ikirarin da ke nuna cewa, kasar Mali na da wani shirin tsaro mai zaman kansa. “Mali na da hadin gwiwar kasa da kasa da Rasha, kuma hadin gwiwa ne na dogon lokaci. Bugu da kari, muna fatan dukkan abokan huldar Mali za su mutunta zabin kasar. Mali na da zabinta ne bisa la’akari da damuwarta, kamar yadda Jamus ta yi nata zabi bisa ga damuwarsa.” An kashe dubban sojoji da fararen hula tare da tilastawa dubban daruruwan mutane barin gidajensu. Ana kuma zargin sojojin Mali da ba su da isassun kayan aiki da cin zarafi a lokacin kazamin rikici. Ya kara da cewa Baerbock bata yi adalci ba, da ta kwatanta abubuwan da suka faru a Mali da Ukraine. “Mali na son yin aiki tare da dukkan abokan huldar ta, da suka hada da Jamus, Rasha, Sin, Amurka, da dukkan abokan huldar da ke son mu hada hannu don ci gaba da kasancewa tare da”
Akwai zargin cewa sojojin Mali tare da hadin gwiwar mayakan kasashen waje — sun kashe daruruwan fararen hula a karshen watan Maris. Kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta kakabawa kasar Mali takunkumi, ciki har da takunkumin kasuwanci, saboda jinkirin komawa mulkin farar hula.