Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bayyana Ranar Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin 15 da 18 ga wannan wata na Afrilu a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Ista na wannan shekara.
Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr. Shuaib Belgore ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. A cewarsa, ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya bukaci mabiya addinin kirista da su yi koyi da halayen hakuri, yafiya, kyautatawa, tawali’u, soyayya, zaman lafiya da hakuri, wadanda Yesu ya koyar. Aregbesola ya yi kira ga Kiristoci da su yi amfani da bikin Ista na bana wajen yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da kuma ci gabanta. Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta bar komai ba wajen magance yawaitar sace-sacen mutane, ‘yan fashi da sauran laifuka. laifin da makiya kasar ne ke aikatawa a sassan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *