Harin ‘yanbindiga: An hallaka wani Hakimi a cikin Masallaci a Taraba

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a garin Maisamari da ke karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba, inda suka kashe wani hakimi mai suna Alhaji Abdulkadir Maisamari.
Shaidun gani da ido sun ce, an kashe Hakimin ne a lokacin Sallar Isha’i a daren ranar Litinin da ta gabata.
Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun bude wuta ne nan take suka kutsa cikin masallacin. An ce mazauna garin sun yi Allah wadarai da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani dutse da ke kusa da garin.
Wani mazaunin garin mai suna Musa Sale ya shaida wa jaridar Aminiya cewa, “wasu jajirtattu ne suka tunkari ‘yan bindigar da suka gudu. Ya ce, babu wanda aka sace, kuma an binne hakimin gundumar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.” Wannan lamari da ya faru na garin Maisamari, ya kawo adadin masallatan da aka kai ma hari a jihar Taraba zuwa uku a makonnin da suka gabata.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi karin haske a kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *