Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina ta bayyana sakamakon zaben shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli da aka guudanar a kananan hukumomi 31 daga cikin 34 na jihar
Sakataren hukumar zaben Lawal Hassan Faskari ne ya bayyana sakamakon zaben a shelkwatar hukumar dake birnin Katsina
Kamar yadda ya bayyana Jam’iyyun siyasa goma sha biyu ne suka fafata a zaben inda jam’iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomi 31 da aka kammala, yayin da ake jiran sakamakon kananan hukumomin Funtua da Daura,inda kuma aka soke na karamar hukumar Dutsinma
Lawal Faskari ya kara da cewa a dukkanin kananan hukumomin wadanda Jam’iyyar ta APC ta lashe zaben ta kuma samu nasarar dukkanin kansilolin da aka kammala zaben su
Ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali tare da yabama dukkanin masu ruwa da tsaki da suka bada gudummuwa wajen samun nasarar zaben a fadin jihar
Sai dai,sakataren hukumar ya bayyana cewa an soke zaben karamar hukumar Dutsinma biyo bayan fuskantar wasu matsaloli yayin gudanar da zaben
Yana mai cewa ana jiran isowar sakamakon na kananan hukumomin Daura da Funtua a lokacin da ake bayyana sakamakon