Yanzu haka dai Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na Najeriya Chris Ngige, yana ganawa da mambobin kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, a Abuja.
Taron wanda aka fara da misalin karfe 5 na yammacin ranar litinin, mai yiwuwa ya sa daliban jami’ar su koma makaranta. Haka kuma taron yana cikin wani mataki na karshe da gwamnatin tarayya ta dauka na kawo karshen yajin aikin da kunhiyar ASUU ke ci gaba da yi. Kungiyar ta fara yajin aikin na baya bayan nan ne a ranar 14 ga watan Fabrairu kafin ta kara wa’adin watanni biyu. Duk da sukar da kungiyar ta ASUU ta sha, ta dage cewa yajin aikin zai ci gaba har sai gwamnati ta amince da bukatu da ke damun kungiyar.