Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar Litanin a matsayin ranar hutu

Gwamna Aminu Bello Masari ya ayyana ranar Litinin 11 ga Afrilu, 2022 a matsayin ranar hutu don baiwa ma’aikata iyalansu damar gudanar da ayyukansu a zaben kananan hukumomi da za a yi a ranar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka raba ma manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakatare na ofishin gudanarwa na shugaban ma’aikatan Alhaji Usman Isyaku.
Sanarwar ta ce, an ayyana ranar hutun ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati da iyalansu damar kada kuri’unsu a mazabunsu. Don haka ssanarwar ta bukaci Ma’aikata da su yi amfani da wannan damar wajen gudanar da ayyukansu cikin lumana, ta hanyar zaben ‘yan takarar da suke bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *