Dan shekara 14 ya nutse a ruwa a jihar Kano

 

Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro dan shekara 14 mai suna Musa Sani, bayan nutsewa a cikin rafi da aka fi sani da Rafin Mukugara, a kauyen Kumbagawa da ke karamar hukumar Karaye jihar Kano.

A wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a jiya Juma’a da safe. “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara na Karaye da misalin karfe 08:00 na safe, daga wani mai suna Abdulbaki Abubakar. Mun aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 8:05 na safe,” inji shi. Ya kara da cewa, an ceto wanda abin ya shafa a some kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.” Abdullahi ya ce, daga baya an mika gawarsa ga Hakimin Karaye  Suraja Magaji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *