A jiya Juma’a ne gwamnatin jihar Kogi tashawarci jama’a da su kauce ma ta’ammuli da naman shanu har na tsawon kwanaki bakwai bayan bayar da umarnin binne gawarwakin wasu shanu 20 da aka gano guba ta kashe a ranar Laraba a Lokoja.
Wani jami’i a jihar ya bayyana cewa, “Abin da gwamnati za ta iya binnewa a yau,wani adadi ne na shanun da abin ya shafa, ba dukkansu ba,”.
Kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) a jihar Kogi Mista Suleiman Mafara, ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Lokoja.
“Bangaren Agro Rangers na rundunar, tare da sashen kula da kiwon dabbobi na ma’aikatar gona, da kuma hukumar kula da tsaftar muhalli ta ma’aikatar lafiya, sun gudanar da gwajin tantance gawarwakin shanun.
“Sakamakon gwajin ya nuna cewa, gawarwakin na dauke da abubuwa masu guba da ba za a iya ci ba, kuma ba su dace mutum ya ci ba.
“Saboda haka, gwamnati na shawartar mazauna jihar Kogi, musamman a Lokoja, inda lamarin ya faru, da su guji cin naman shanu nan da kwanaki bakwai masu zuwa,” in ji shi.
Madara ya tabbatarwa da jama’a cewa, jami’an rundunar da sauran jami’an da abin ya shafa, suna yin duk mai yiwuwa don kwantar da hankaula akan duk wata barazana da ka iya tasowa daga wannan lamari marar dadi.
Ya ce rundunar ta aike da tawagogin sa ido da ke ci gaba da kwantar da hankula a muhallin. da kuma jami’an da ke yaki da duk wata barazana don kawar da halin da ake ciki.
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban sashin Agro Rangers na hukumar NSCDC reshen jihar, Mista Bayode Emmanuel, ya ce, kungiyar mahauta a kasuwannin, sun gudanar da bincike da kuma duba gawarwakin shanun da aka binne.
Emmanuel ya bayyana cewa, gawarwakin shanun da aka karbo, an yi ne bisa tsarin da aka tsara kafin a binne su wanda duk masu ruwa da tsaki suka tabbatar da su.
Kamfanin dillancin labarai na najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar Alhamis Dokta Salau Tarawa, Daraktan Kula da Dabbobi na Ma’aikatar Gona ta jihar Kogi, ya shawarci mazauna garin da su guji mu’amala da naman shanu na akalla mako guda, domin akwai yiwuwar wadancan shanu 20 sun sha guba a lokacin da suke kiwo.