Wata fashewa a jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta kashe mutum takwas tare da jikkata uku

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwairo Kakakin gwamnatin Kongo Patrick Muyaya yana sanar da cewa, wata fashewar wani abu da ta afku a wata mashaya a sansanin soji da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ta kashe mutane takwas tare da jikkata wasu mutum uku a yau Alhamis.
Ba a dai bayyana musabbabin faruwar lamarin a sansanin Katindo da ke birnin Goma ba. An tura jami’ai domin gudanar da bincike, in ji Muyaya a bayanin da ya wallafa a shafin Twitter. “An bukaci jama’a da su kwantar da hankula, yayin da ake jiran rahotonda zai ba mu damar fahimtar yanayin wannan bala’i,” in ji shi. Sojojin Kongo na fafatawa da kungiyoyin ‘yan tawaye da dama a gabashin kasar da ke fama da rikici. Kawo yanzu dai babu wata alamar da ta nuna cewa hari ne ya haddasa fashewar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *