An ba hambararren shugaban Burkina Faso damar komawa gida daga inda yake tsare

A cikin wata sanarwa da gwamnatin Burkina Faso ke jagoranta ta ce tsohon shugaban kasar Kabore zai koma gidansa bayan an tsare shi a gida.

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, wanda aka yi ma daurin talala tun bayan hambarar da shi a wani juyin mulki a watan Janairu, an ba shi damar komawa gidansa na kashin kansa, a cewar gwamnatin mulkin soji.
Bayan shafe makwanni uku ana tuntubar juna, an yanke shawarar cewa Kabore zai iya komawa gidansa da ke Ouagadougou, babban birnin kasar, wanda jami’an tsaron gwamnati za su ba da kariya, in ji kakakin gwamnatin mulkin soja Wendkouni Joel Lionel Bilgo a cikin wata sanarwa.
Ba a dai san ko wane ne daga cikin gidajen da yake da su yake ciki ba, kuma da alama har yanzu ana tsare da shi.
An ba Kabore damar ganin dangi da abokai na kud da kud, kuma an ba shi damar ya yi amfani da wayarsa, amma ba a ba shi izinin yin tafiya a waje da gidansa ba, kamar yadda wasu mambobin gwamnatin mulkin soja biyu suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *