Ba nufin mu ba ne karbar kudin fansa- maharan jirgin kasa

Masu garkuwa da fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna sun ce,
ba manufarsu ce su karbi kudin fansa daga Gwamnatin Tarayya ba, suna masu cewa ba sa son kudi.
A wani faifan bidiyo da maharan suka fitar a jiya Laraba, ‘yan bindigar sun bayyana cewa, gwamnati ta san abin da suke bukata, kuma sun yi barazanar kashe wadanda suke a hannunsu idan ba a biya musu bukatunsu ba.
Bidiyon an yi shi ne biyo bayan sakin Manajan Darakta na Bankin Noma, Mista Alwan Hassan.
Daya daga cikin ‘yan fashin da ya yi magana da harshen Hausa, ya ce, an sako manajan Daraktan ne saboda shekarunsa da kuma wannan wata na Ramadan. “Mu ne kungiyar da ta yi awon gaba da fasinjoji a cikin jirgin. Daga cikin su akwai wannan mutumi da ya rika rokonmu saboda tsufansa kuma muka ji tausayinsa saboda watan Ramadan, don haka muna so mu mayar da shi ga iyalansa,” inji mai magana a faifan bidiyon.
Wani dan fashin da ke sanye da kakin soji, ya amince da abin da shugabansu ya ce, kuma ya bukaci gwamnatin tarayya da kada ta bibiye su, idan ba haka ba, za su kashe wadanda ke hannunsu. Ya ce, “Ina son nanata cewa, abin da ya fada gaskiya ne. Kada ku yi ƙoƙarin binciko mu nan ko ku cece su, domin kashe su ba shi ne gabanmu ba. “Ba ma son kudin ku, da muna son kudi, da ba mu kai harin ba. Kun san abin da muke so”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *