Gwamnatin Jihar Katsina ta karyata labarain dake yawo a wasu kafafen yada labarai musamman na zamani ciki harda gidan talabijin na Channels da kuma Jaridar Leadership dake nuna cewa akwai barkewar matsalar tsaro a jihar.

Labarin ya nuna cewa akwai wasu mutane 34 yan asalin jihar Akwa Ibom dake zaune a Karamar Hukumar Jibia a Katsina wadanda gwamnatin jihar Akwa Ibom ta turo da motoci aka kwashe su a sakamakon rashin tsaro.

A taron manema labarai da ya gudana a Cibiyar Yanjarida dake sabon gidan gwamnatin Katsina, Jami’an Gwamnatin Jihar da su ka hada da Al_Amin Isah, Darakta Janar Na Sabbin Kafafen Yada Labarai da Ibrahim Ahmad Katsina, Mai Taimakawa Gwamna Kan Sha’anin Tsaro sun bayyana cewa mutanen da aka kwashe sunyi haka ne da manufar tada hankalin al’umma da kuma karbar wani abu daga hannun gwamnatin jihar su.

Jami’an Gwamnatin Jihar Katsinan sun bayyana cewa batun tsaro a jihar ya inganta domin ana samun ci gaba, sannan sun bukaci gwamnatoci da subi a hankali su binciki labari kafin daukar mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *