‘Yan sanda sun ceto mutane 13 tare da kashe wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta ce ta ceto mutane 13, tare da harbe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai da yammacin jiya Lahadi a garin Warri, ya kuma kara da cewa, tunfunar ta samu bindiga kirar AK-17 guda daya daga hannun wanda ake zargin. Edafe ya ce, an harbe wanda ake zargin ne a ranar Lahadin 3 ga watan Afrilu, ta hanyar hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan da ke aiki a sashin Ogwashi-Uku da kuma ‘yan banga na yankin.
Ya bayyana cewa, wanda ake zargin tare da tawagarsa sa sun tare wata motar bas mai daije da mutane 14 a unguwar Aniagbala ta hanyar Ubulu-Uku express a karamar hukumar Aniocha ta kudu. “A yau, 3 ga Afrilu, 2022, da misalin karfe 0840,rundunar ‘yan sandan ta samu bayanai fake cewa, wasu gungun masu garkuwa da mutane sun kama wata motar bas mai kujeru 14 mai lamba: M831-FJK. “An kama motar bas din ne a unguwar Aniagbala ta hanyar Ubulu-Uku express a Aniocha ta Kudu. An sace 13 daga cikin fasinjojin aka kai su daji,” in ji shi.
Edafe ya ci gaba da cewa, da samun labarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta, Mista Ari Ali, ya umurci DPO na yankin Ogwashi-Uku da su jagoranci jami’ai zuwa cikin dajin, tare da tabbatar da cewa an kama wadanda ake zargin sannan da ceto wadanda lamarin ya rutsa da su. “Bisa umarnin, DPO, CSP Mohammed Naallah, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga cikin gaggawa zuwa cikin dajin tare da fatattakar ‘yan bindigar. ” “A yayin da ake musayar harbe-harbe, daya daga cikin wadanda ake zargin da aka harba, ya mutu nan take yayin da sauran ‘yan tawagar suka tsere da raunukan harbin bindiga,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce an ceto dukkan mutanen 13 da aka yi garkuwa da su da ransu ba tare da sun ji rauni ba, ya kara da cewa, ana ci gaba da sa ma daji ido da nufin kamo sauran ‘yan tawagar da suka gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *