Hadarin mota ya ci rayokan yara 2 a jihar Osun

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), reshen jihar Osun, ta ce wasu yara mata biyu sun rasa rayukansu jiya Lahadi, a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Ipetu-Ijesa/Ilesa. Kwamandan sashin, Mista Paul Okpe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Malama Agnes Ogungbemi, ta fitar a Osogbo. Okpe ya ce hatsarin ya afku ne a tazarar kilomita bakwai daga mahadar Iwaraja da misalin karfe 2.44 na rana, wanda ya hada da wata babbar mota kirar Howo Sino da kuma wata motar bas kirar Nissan. Hatsarin ya rutsa da maza uku da yara mata uku, inda mata biyu suka rasa rayukansu, yayin da sauran fasinjojin suka sami rauni.
“Haɗarin ya faru ne sakamakon gudu da fashewar taya da kuma rashin bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa da masu ababen hawa ke yi,” in ji kwamandan sashin.
A cewarsa, an samu fashewar taya a daya daga cikin motocin abin da ya haifar da rasa natsuwa kafin hatsarin ya faru. Ya ce an kai gawarwakin a dakin ajiyar gawa na Asibitin Wesley Guild da ke Ilesa, yayin da wadanda suka jikkata aka kai su asibiti domin yi musu magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *