Kungiyar matasan Arewa ta marama kudurin gwamnan Kaduna baya

Kungiyar tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF), ta marawa gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai baya akan kudurinsa na dauko sojojin haya na kasashen waje domin yakar ‘yan bindiga a jihar. Shugaban kungiyar na kasa, Yerima Shettima ya ce, kamata ya yi gwamna El-Rufai ya hada da sojojin haya na kasashen waje idan irin wannan matakin shi ne zai kare mazauna Kaduna. Gwamna El-Rufai dai ya sha alwashin kawo sojojin haya daga kasashen waje idan har gwamnatin tarayya ta kasa magance ta’addanci da rashin tsaro a jihar baki daya. Sai dai shugaban kunviyar ta tuntuba Shettima ya bayyana a yahin wata tattaunawa da jaridar DAILY POST cewa, idan har matakin gwamna El-Rufai zai kawo sakamakon da ake bukata, to ya ci gaba. Ya ce: “Ina goyon bayan hakan gaba daya domin aikin gwamnan ne ne ya kare ‘yan jihar Kaduna bisa tsarin mulki. Don haka, idan har yana jin ba zai iya aminta da jami’an tsaronmu ba sakamakon sulhun da suka yi ta wata hanya, to babu dalilin da zai hana a dauko na haya. “Kuma a kan wannan, ina goyon bayansa gaba ɗaya kuma na yarda da shi.” In ji Shettima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *