Masari Ya Bukaci Gudummuwar Malaman Addini Wajen Inganta Tsaro Da Zaman Lafiya A Jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bukaci Malaman Addini da su sanya jihar cikin addu’o’i domin samun zaman lafiya a fadin jihar

Ya bukaci hakan ne a wajen taron karama juna sani da aka shiryawa malamai da limamai hadi da shugabannin al’umma kalkashin ofishin mai bashi shawara akan sha’anin tsaro Ibrahim Katsina

Gwamnan wanda kwamishinan harkokin addini na jihar Malam Isah Lawal Doro ya wakilta a wajen taron ya bukace su da suyi amfani da abubuwan da suka tattauna a wajen taron a lokutan karatun su na tafsiri da lokutan karantar da almajiran su domin cimma nasarar da ake bukata

“Kuyi kokari kuyi amfani da abinda aka tattauna anan,hakan zai taimakemu al’ummomin da kuke karantarwa su zama mutane na kwarai, kuma kune ruwan kashe wutar fituttunan da suka addabe mu,da yardar Allah ta hanyar addu’o’i daga bakunan ku da na almijaran ku masu albarka zamu samu zaman lafiya a jihar nan”.

A nasa jawabin mai ba gwamnan shawara akan sha’nin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina ya bayyana cewa an shirya taron bitar ne domin karama juna sani a tsakanin mahalartan domin inganta kokarin da gwamnatin jihar keyi na samar da tsaro a da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar

Ya jaddada bukatar da ake da ita ga mahalartan na su bada gudummuwar su wajen cimma nasarar shirin gwamnatin na inganta zamantakewa dake da mahimmanci ga zaman lafiya mai dorewa a cikin al’ummar

A lokacin taron an gabatar da kasidu domin karama juna sani wajen inganta hadin kai da zamantakewa dake da tasiri ga samuwar tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *