Harin jirgin kasa babban abin ban tsoro ne-gwamnonin Arewa

Kungiyar gwamnonin Arewa, ta bayyana harin jirgin kasa da ya rutsa da fasinjoji 970 a jiya Litinin a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da ‘yan ta’adda suka kai a matsayin ‘babban abu da ban tsoro’.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da shugabanta kuma gwamnan Filato, Mista Simon Lalong ya fitar, ya bayyana  fusatarsa da alhini a kan harin.

Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na gwamnan, Dr. Makut Maham ne ya sanar da hakan a yau Talata a Jos.

Kungiyar ta yi Allah wadai da harin inda rahotanni suka ce, ‘yan ta’adda sun yi amfani da bama-bamai wajen tarwatsa hanyar jirgin kasa, daga Abuja zuwa Kaduna, inda aka kashe wasu fasinjoji da jikkata wasu, tare da yin garkuwa da wasu.

“Gwamnoni da al’ummar yankin da ma sauran ‘yan Najeriya, sun damu matuka game da mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa matafiya, wadanda ke nuna rashin mutunta rayukan mutane da kuma tausayi.”

“kungiyar gwamnonin tana jajantawa iyalan wadanda aka kashe da wadanda aka sace ko aka jikkata.”

Gwamnan Ya yi Allah-wadai da wannan ta’addancin baki daya, sannan ya yaba wa sojojin da suka yi gaggawar shiga lamarin wanda ya dakile faruwar lamarin.

“Saboda haka gwamnonin Arewa suna karfafa gwiwar jami’an tsaro, da su kara zage dantse wajen aikin ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da bata lokaci ba. Sannan kuma a kama ’yan ta’addan da suka gudu tare da gurfanar da su a gaban kotu.”

“Kungiyar tana aiki tare da gwamnatin tarayya da Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna, don ganin an magance wannan lamari da sauran hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan da aka yi a jihar.”

kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su tallafa wa jami’an tsaro wajen gudanar da bincike da kuma wajabcin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ta hanyar ba da bayanan da suka dace game da masu aikata laifuka a yankin da kuma kasar.

Ya ce, gwamnatocin jihohin yankin sun kara zuba kudi a fannin tsaro tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, domin kara karfin jami’an tsaro.kungiyar gwamnonin ta kuma yaba da tausayin da ‘yan Najeriya suka nuna wajen bayar da gudummawar jini ga wadanda suka jikkata a halin yanzu, a cibiyoyin lafiya daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *