‘Yan bindiga sun kashe mutane 5, tare da jikkata 3 a jihar Filato

Rahotanni sun ce, wasu ‘yan bindiga a jiya Litanin, sun kashe mutane biyar tare da raunata wasu uku a al’ummar Iregwe da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Mista Davidson Malison, sakataren yada labarai na kungiyar ci gaban Iregwe na kasa, ya bayyana haka a yau Talata a Jos cewa, an kai rahoton harin ga ‘yan sanda da sojoji a jihar.

Malison ya bayyana cewa, maharan sun kai harin ne cikin dare, inda suka kashe tare da raunata wadanda suka mutu, sun kuma lalata wata mota tare da kwashe wasu babura.

ya kuma kara da cewa wadanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawa a asibiti.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Ogaba, kan batun, ya tabbatar da cewa, an kai rahoton harin ga ‘yan sanda.

Ogaba ya tabbatar da cewa, ‘yan sanda za su fitar da sanarwa kan lamarin.

Maj. Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Safe Haven’, runduna ta musamman dake wanzar da zaman lafiya a jihar Filato da kewaye, ya ce, “Bani da cikakken bayani.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *