Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja,da mai shari’a Emeka Nwite ke jagoranta,ta ki amincewa da bukatar bada belin DCP Abba Kyari da aka dakatar, da wasu da aka gurfanar a gaban kotun bisa zargin su da safarar miyagun kwayoyi.
A cewar kotun, zarge-zargen da ake yi wa wadanda ake tuhuma na da nauyi, kuma ya kamata a hana bada su beli domin a yi adalci.
“Tuhumar da ake yi masu na da karfi. Masu gabatar da kara sun yi bayani da kakkausar murya kan dalilin da ya sa a hana su beli. Na yi la’akari da bukatar da aka gabatar a gabana da kuma gabatar da lauyoyi, an ki neman belin masu nema na 1 da na 2 ne, domin neman adalci da kuma al’umma,” inji kotun.