‘Yan bindiga sun kai hari a ofishin ‘yan sanda na Imo

Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su waye ba, a ranar Litinin , sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Otoko da ke karamar hukumar Obowo a jihar Imo, inda suka raunata wasu ‘yan sanda biyu.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida ma jaridar leadership cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki ofishin ne da misalin karfe 3 na dare, suna harbe-harbe, lamarin da ya sa mazauna garin suka firgita.

Majiyar ta ce, “Ba wanda ya runtsa. Tun da sanyin safiyar ranar Litinin, an yi ta musayar wuta da fashe-fashe wanda na tsawon lokaci, kowa na cikin fargabar. Sai dai zaratan jami’an ‘yan sanda sun shiga cikin maharan tare da yin turjiya.

“bayan tsagaitawar harbe-harben, wasunmu sukayunkura muka je, muka tabbatar da abinda ya faru, abin farin ciki ne ganin yadda ofishin ya kasance, domin ‘yan sanda sun iya jure harbin, duk da cewa mun ga ‘yan sanda biyu sun samu munanan raunuka.”

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Michael Abattam, ya tabbatar da faruwar harin duk da cewa ba a rasa rayuka ba.

Abattam ya ce: “Baya ga ‘yar barnar da aka samu a sansanin ‘yan gudun hijira da wata mota, ba a samu asarar rai ba. Sai dai an yi wa dan sandan da ya samu rauni magani.”

kakakin ya yi kira ga jama’a da su bayar da sanar da rundunar duk wanda aka san yana da maganin raunukan harsashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *