‘Yan jarida da dama na kasar Tunisia, sun gudanar da zanga-zanga a jiya Juma’a domin neman ‘yancin ‘yan jarida da kuma neman a sako wani dan jarida da aka tsare saboda ya ki bayyana majiyoyinsa ga hukumomi.
Masu zanga-zangar sun taru a wajen ofishin kungiyar ‘yan jarida ta kasa ta SNJT, suna rera take da bayyanma cewa, aikin jarida ba laifi ba ne, tare da zargin hukumomi da takurawa kafafen yada labarai, tun lokacin da Shugaba Kais Saied ya kwaci mulki a watan Yulin shekarar 2021.
Wani mai zanga-zangar ya rike allunan da ke cewa,”’yancin ‘yan jarida jan layi ne”.
Wakilin babban gidan rediyon kasar, Mosaique FM Khalifa Guesmi, an kama shi ne a ranar 18 ga Maris a karkashin dokar yaki da ta’addanci, bayan da ya ki bayyana majiyar sa, kan labarin wargajewar wata kungiyar ‘yan ta’adda.
Shi da wasu ‘yan jarida biyu na Mosaique FM, da suka hada da babban editan Houcine Dabbabi, sun bayyana a gaban wata kotun yaki da ta’addanci da safiyar ranar Juma’a.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta SNJT Mahdi Jlassi, ya bayyana kamen Guesmi, a matsayin hari mafi muni da aka kaiwa ‘yancin ‘yan jarida, tun bayan juyin juya halin da ya faru a kasar ta Arewacin Afirka a shekarar 2011.
A watan Yulin da ya gabata, Shugaba Kais Saied, ya dakatar da majalisar tare da kwace madafun iko.
Tun daga lokacin ya koma kan mulki bisa doka tare da kwace iko da bangaren shari’a, yayin da ya sha alwashin kare ‘yancin da aka samu a juyin juya halin shekara ta 2011, wanda ya hambarar da mulkin kama karya na Zine El Abidine Ben Ali.
Kasa da mako guda da kama Guesmi, jami’an ‘yan sanda sanye da kayan sarki, sun hana wasu ‘yan jarida biyu watsa labarai a zanga-zangar neman a gudanar da bincike kan bacewar wani matashi dan shekara 19 mai suna Omar Labidia a shekarar 2018, bayan da ‘yan sanda suka yi zargin nutsar da shi cikin kogi.