A jiya Juma’a ne shugabannin kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka, suka gudanar da wani taro kan rikicin siyasar kasar Mali, watanni uku bayan kakaba wa al’ummar yankin Sahel takunkumi mai tsauri.
An bude kofar tattaunawar da aka yi a Accra babban birnin Ghana, bayan rufe kofofin tsakanin shugabannin kasashen. Ministan harkokin wajen Mali Aboudlaye Diop ya tabbatar da ganawar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter. Haka kuma a tattaunawar da aka yi akan halin da ake ciki a kasashen Guinea da Burkina Faso, inda su ma aka yi juyin mulki a baya-bayan nan.
Taron dai na zuwa ne kimanin mako guda bayan da wakilin ECOWAS, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a kasar Mali, ya yi tattaki zuwa Bamako amma tattaunawar maido da mulkin farar hula ba ta cimma nasara ba. Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS mai kasashe 15, ta bukaci sojojin Mali da suka kwace mulki a shekarar 2020, su shirya zabe cikin watanni 12-16.
Ya zuwa yanzu, shugaban mulkin soji, Assimi Goita, ya bijirewa matsin lambar kasa da kasa na gudanar da zabe. ECOWAS da UEMOA duk sun sanyawa Mali takunkumin tattalin arziki da diflomasiyya a watan Janairu bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta zartar da ci gaba da mulki har na tsawon shekaru biyar.
A ranar alhamis din da ta gabata ne kotun kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (UEMOA) ta bayar da umarnin dakatar da takunkumin da aka kakabawa kasar Mali. Babu tabbas ko hukuncin dakatarwar da kotun UEMOA ta yanke zai kai ga dage takunkumin nan take. Hukumomin mulkin sojan Mali na kallon takunkumin a matsayin wanda ya sabawa doka tare da sha alwashin kalubalantarsa a kotunan duniya.