Babban kwamitin tsakaiya na APC ya amince da nada shugabannin shiyyar Kudu maso kudu

Babban kwamitin tsakiya na jam’iyyar APC, ya zabi shugabanni, kafin taron jam’iyyar a ranar Juma’a. Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a shiyyar Kudu-maso-Kudu sun amince da nada tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Victor Giadom,  a matsayin dan takarar shugabancin kwamitin aiki na kasa. Sauran ‘yan takarar da aka zaba sun hada da kwamishinan lafiya na jihar Delta, Dr Betta Edu da Mista Felix Morka.
Wata sanarwa da masu ruwa da tsakin suka fitar ta ce, an dauki mambobin jam’iyyar uku ne a taron masu ruwa da tsaki na karshe da aka gudanar a Abuja. A jerin sunayen da masu ruwa da tsakin suka sanyawa hannu akwai, Mista Victor Giadom a mataimakin shugaba a Kudu-maso-Kudu da Dr Betta Edu a shugabar mata ta kasa, da kuma Dr Felix Morka a matsayin sakataren yada labarai da wayar da kai. Jerin sunayen wadanda aka nada a matsayin wadanda aka amince da su, na dauke da sa hannun Gwamna Ben Ayade da Sanata John Akpanudoudehe da Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da Ministan Neja-Delta, Sen. Godswill Akpabio. Sauran sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole; tsohon karamin ministan noma, Heineken Lokpobiri da tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Lucky Imasun. Haka kuma a wajen taron akwai manyan jihajigan jam’iyyR da dama.
Mrs Stella Okotete, wakiliyar mata a kwamitin riko na musamman; wakilin Kudu maso Kudu Mista David Lyon; Sen. Ita Enaga, Sen. Magnus Abe, Mr Victor Giadom da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sen. Ovie Omo-Agege.sauran su ne, Mataimakiyar shugaba ta kasa ta Kudu-maso-Kudu tana shiyyar zuwa jihohin Rivers/Bayelsa, shugabar mata ta kasa zuwa jihohin Akwa Ibom/Cross River da Sakatariyar Yada Labarai ta Kasa na Jihohin Edo/Delta. Yayin da Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya zabi Betty Edu (Cross River) a matsayin shugabar mata ta kasa, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, ta zabi Victor Giadom  (Jihar Rivers) a matsayin mataimakiyar shugabar kasa. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya zabi Dokta Felix Morka (Jihar Delta) a matsayin Sakataren Yada Labarai na Kasa,” inji sanarwar.
A halin da ake ciki, wasu masu neman takara sun sami fom ɗin nuna sha’awar tsayawa takarar. Misali, Mary Ekpere Eta, tsohuwar Darakta Janar ta Majalisar Cigaban Mata ta Kasa (NCWD) da Misis Helen Boco Effiom sun samu fom din tsayawa takarar kujerar shugabar mata ta kasa. Haka kuma, tsohon mataimakin sakataren yada labarai na kasa, Yekini Nabena, ya samu fom din tsayawa takarar mataimakin shugaba na Kudu maso Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *