A jiya Alhamis ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi fatali da karar da bangaren da Sanata Abubakar Gada ke jagoranta ya shigar kan rashin ikon yanki.
Idan dai za a iya tunawa, ana ci gaba da takun saka a jam’iyyar ta APC a Sokoto, tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Abubakar Gada.
A baya dai wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta ki amincewa da bukatar wani bangare na jam’iyyar ta APC a jihar Sokoto, da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar Aliyu Wamakko, na a yi watsi da hukuncin da ta yanke a baya, kan zabukan da aka yi a jihar.
Sai dai bangaren Wamakko ya daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.
Shugaban jam’iyyar na jiha, Isa Sadiq Acida ne ya gabatar da karar.
Tun da farko, Acida ya bukaci wata babbar kotu da ke Sokoto da ta hana jam’iyyar APC amincewa da Mainasara Abubakar Sani da sauran su, a matsayin shugabanni da wakilai na kananan hukumomi da na jahoha na jam’iyyar da aka gudanar a ranakun 13 ga Oktoba da 14 ga Satumba da 16 ga Oktoba na 2021.
Da yake yanke hukunci kan karar da bangaren Gada ya shigar, dan kwamitin alkalai, H.S Tsammani da B.A. Georgewill da D.S Senchi gaba daya sun gabatar da cewa, babbar kotun tarayya ba ta da hurumin yanki, kuma ta yi watsi da daukaka karar.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, Dr.Hassan Liman (SAN),lauyan Hon. Isa Sadik Acida, Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, ya ce, “za mu tabbatar da cewa, kungiyar NBA ta kula domin ganin hakan bai sake faruwa ba”.