tare da rahoton BBC
Shugaban Amurka Joe Biden na Brussels domin halartar taron tattaunawa kan rikicin kasar Ukraine da ya tsananta.
Batun tsaro da takunkumi da kuma lamarin ‘yan gudun hijira na Ukraine, su ne kan gaba a jerin abubuwan da shugabannin na kungiyar NATO da Tarayyar Turai da kuma kungiyar manyan kasashe masu karfin masana’antu ta G7 za su tattauna a yau. Kuma manufar taron ita ce ta nuna cewa, kan kasashen yamma a hade yake.
Shugaban na Amurka ya je Turai ne cike da fatan nuna hadin kan kasashen yamma a lokacin da tsaron nahiyar ke cikin barazana fiye da yadda ya kasance a gomman shekarun baya.
A taron na ranar Alhmis na kawancen tsaro na NATO, shugabanni sun shirya sanar da samar da ƙarin karfi na soji ga kasashen gabashi da kuma tsakiyar Turai, wadanda ke ganin suna cikin barazanar Rasha.