SHARHI KAN SAMARDA SABON BIRNI DA MA’AIKATAR KASA DA SUFIYO TA JAHAR KATSINA ZA TA YI.

Kundin tsarin mulkin Nijeriya bai yi shinge a kan cewar sai wanda ya kware a Ma’aikata ko Sashen da zai rike ba idan aka nada shi a matsayin memba na majalisar zartaswa a matakin Jaha ko Tarayya,sai dai idan aka yi gam-da-katar abin ya fi haifa da mai ido
Ma’aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina na daga cikin wuraren da suka dace da kwararren Jami’in Tsara Birane(Town Planner) da ke shugabantar Ma’aikatar. Tpl. Usman Nadada.
Wannan dama da Tpl.Usman Nadada ya samu bayan shekarun da ya dauka yana aiki mai alaka da tsara birane tun bayan kammala karatunsa na digiri na daya da na biyu,wanda har ya kai shi ga rike kujerar Janar Manajan Hukumar Tsara Birane da ‘Yankuna na Jahar Katsina na tsawon shekaru ya sanya yake da ra’ayi na ganin cigaban harkokin da suka jibanci Kasa da Sufiyo.
Kudurori da Manufofin da Tpl.Usman Nadada ya hau mikamin kwamishinan Ma’aikatar da su na tunanin dorawa daga inda wanda ya gada ya tsaya a kan inganta tsarin Kasa sune sirrin nasarorin da ake kudurin samu
Wannan tsari kuwa shi ne,sarrafa Kasa kai tsaye a maimakon rarrabawa ba tare da sarrafawa ba. A karkashin wannan tsari ne aka yi tunanin samarda wani sabon birni da zai kunshi kayan more rayuwa dabam-daban da mutanen da za a haifa a sabuwar duniyar za su amfana da su.
Wannan sabon birni da za a kafa a Arewacin garin Katsina, a kan hanyar Katsina zuwa Jibia an rada masa suna’KATSINA RACE COURSE VILLAGE’
Idan wannan birni ya kammalu zai kunshi Gidaje, Makarantu,Massallatai gami da Filayen Wasanni dabam-daban, musamman na Wasannin tseren Dawaki da na Kwallon Dawaki.
Shedar yiwuwar wannan aiki tuni Ma’aikatar Kasa ta yi yarjejeniya da wani kamfanin tuntuba na wasu kwararrun masu ilmin tsara birane mai suna’BIN-HAJJ CONSULT’ da ya samarda taswira ta zahiri da bayyana kwarangal din birnin baki daya
Tuni wannan taswira ta samu sambarka da amincewar Maigirma Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Maimarbata Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da sauran masu ruwa da tsaki
Wani abun da ya kamata mutane su sani shi ne tuni an fara rattabawa takardun yarjejeniyoyi hannu da kamfanonin da ke huldar samar da muhalli(Developers) don cigaba da tabbatuwar samuwar wannan sabon birni
Irin wannan shirye-shirye wadanda duniyar cigaba suka yi nisa ga aiwatar da su,a kasashe irin namu na ifrikiyya ba a cika samun aiwatar da su dari bisa dari ba.
Don haka, kaifin basira da hikima ta Kwamishinan Kasa da Sufiyo a Jahar Katsina Tpl.Usman Nadada ya yi amfani da kwarewar da ya ke da ita ta wannan fuska ya hannanta kula da tafiyar ga Kamfanin BIN-HAJJ CONSULT don haka ta cimma ruwa.
Wani sabon salo da Tpl. Usman Nadada ya yi wa wannan aiki tare da shawarar abokan aikinsa da kuma amincewar gwamnati shi ne wannan birni shi zai samarda kansa da kansa.
Yanzu nan da wasu ‘yan lokutta da yardar mai duka sabon birni zai wanzu a nan Katsina,sai dai sanin karkashin wace gunduma zai kasance, muna jiran masana tsare-tsaren iyakoki su bayyanas.
Ko ba komai, ajiye kwarya a bisa gurbinta ta kara tabbata a Ma’aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina

Alkalamin: Yakubu Lawal
Dan Jarida
Jami’in Hulda da Jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *