Mustapha Inuwa yayi taro da kungiyoyi akan takarar sa

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa ya gudanar da taro da kungiyoyi hadi da masu ruwa da tsaki da suka dade suna kiraye gare shi ya fito takarar gwamnan jihar Katsina

Gagarumin taron wanda ya gudana a dakin taro na Katsina Motel na zuwa ne yan kwanaki bayan da sakataren gwamnatin ya mika takardar sa ta neman tsayawa takarar a babban ofishin Jam’iyyar reshen jihar

Daga cikin kungiyoyin da suka halarci taron akwai #Inuwa likemind da Zawiyyah Alheri da K34 da Alheri danko ne da dai sauran kungiyoyi da dama

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban taron kuma mai neman takarar gwamnan jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana cewa taron na da nufin haduwar Sada zumunci hadi da bayyana godiyarsa ga dimbin kungiyoyin da masu ruwa da tsaki da suka dade suka jajirce wajen Kira gare shi ya fito takarar

Kazalika domin gode masu bisa kauna tare da tabbatar masu da amsa kiran da suka dade suna masa da kuma cigaba da shirin dake gaba

Ya bukaci magoya bayan da su maida lamurran su ga Allah tare da kauda kai daga masharranta dake kokarin bata masa suna al’amarin da ya bayyana cewa yarfe ne kawai irin na siyasa

Sakataren gwamnatin ya bukace su da maida hankali wajen fadakar da al’ummar jihar Katsina alheran dake rubuce a littafin tarihinsa tun daga aikin sa na koyarwa a jami’a zuwa shugaban hukumar KSTA da shugaban karamar hukuma har dai ya zuwa kwamishinan Ilmi da ya rike zuwa shugabancin jam’iyya da Sakataren gwamnati da yake rike da shi a karo na ukku a halin yanzu

“Ku zauna da jama’a lafiya kada ku yarda a yi tashin hankali da ku akan Takara ta,
Idan kana son Mustapha Inuwa kada kayi fada da kowa,kayi kokarin fito da alheran da ka sani game dani ba ta hanyar fada ba, wadanda na tabbatar su masharrantan da yan kanzagin su basu yi irin alheran da nayi ba”,Mustapha Inuwa yace.

Ya tabbatar wa kungiyoyin da sauran magoya bayan cewa za’a cigaba da neman goyon bayan jama’a a duk inda suke inda kuma ya bukace su da su cigaba da yin abinda ya dace domin samun hadin kan jam’iyyar APC a cikin gida da kuma a babban zaben 2023 mai zuwa

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe a halin yanzu na bayyana cewa Mustapha Inuwa na samun rinjaye na mahimman masu ruwa da tsaki a sararin siyasar Katsina Inda a majalisar dokokin jihar da kananan hukumomi yake da rinjayen masu ruwa da tsaki

Kamar yadda alkalumman ke nunawa Mustapha Inuwa yana da goyon bayan yan majalisu 18 daga cikin 34 a halin yanzu,yayin da kuma ya samu goyon bayan 20 daga cikin 34 na yan takarar APC na zaben kananan hukumomin da za’ayi a watan Aprilu dake tafe

Kamar kuma yadda aka lura da cewa yana cigaba da samun goyon bayan daruruwan kungiyoyin siyasa da wasu jiga jigan jam’iyyar ta APC a jihar ta Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *