“Zan koma noma idan Buhari ya zabi Tinubu a matsayin wanda zai gaje shi”

Mai ba shugaba Buhari shawara na musamman kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu ya ce, zai koma noma idan shugaba Muhammadu Buhari ya zabi shugaban jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Ojudu ya bayyana haka ne, yayin wata tattaunawa,

A lokacin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa akan abin da zai ce idan shugaba Buhari ya zabi Tinubu a matsayin dan takarar sa. Ojudu ya ce ,ba zai taba yin hakan ba.

Ojudu ya yi ikirarin cewa, ba zai taba iya tallafawa ko aiki da wanda bai yarda da shi ba.

Ya ce, “Ba zan taba goyon bayansa ba. Ka rubuta zan koma gona.”

“Idan ban yi imani da ku ba, ba zan yi aiki tare da ku ko a gare ku ba.”

A halin da ake ciki, Ojudu ya bayyana a baya cewa ba zai goyi bayan burin Tinubu na zama shugaban kasa ba, saboda zabin siyasa na ka’ida, ba cin amana ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *