‘YAN BINDIGA SUN DASA NAKIYA A OFISHIN HUKUMAR ZABE A JIAHR IMO

‘Yan bindiga sun dasa nakiya a ofishin hukumar zabe a Owerri babban birnin jihar Imo inda hakan ya yi sanadiyyar rasa ran dan sanda.

Harin ya lalata motoci da ke ajiye a harabar ofishin kuma ya lalata ofisoshin a ginin duk hukumar zabe daga bisani ta ce harin bai shafi muhimman kayan aikin zabe ba.

Duk da haka jami’an tsaro sun tinkari miyagun irin inda a ka samu musayar wuta da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar dan sandan daya amma su ma ‘yan sandan sun bindige mahara uku.

An ruwaito kakakin ‘yan sanda a jihar Micheal Abattam ya na cewa sun rasa jami’i sannan wani daya kuma ya samu rauni amma sun hallaka uku daga miyagun, su ka cafke biyu kuma su na sa ran kama wasu nan gaba kadan.

An samu bindigogi kirar AK 47, nakiyoyi da boma-boman man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *