Mozambique na karfafa tattaunawar sulhu tsakanin  Rasha da Ukraine

Shugaba Filipe Nyusi na Mozambique ya nace cewa, kasarsa tana karfafa tattaunawa a rikicin Ukraine da Rasha, a lokacin da ya tarbi takwaransa Marcelo Robelo de Sousa na kasar Portugal a jiya Alhamis, a ziyarar kwanaki uku da zai kai kasar dake kudancin Afirka.

Shugaba na Mozambique ya ce, idan har tallafin kasuwanci da na soja, su ne wasu manyan batutuwan da aka tattauna a kai, to rikicin da ya barke a Ukraine shi ma ya zo kan gaba. Shugaba Nyusi ya sake nanata matsayin kasarsa na ‘yar baruwanmu. “Mozambik ba ta goyon bayan yaki. Muna goyon bayan tattaunawa, kuma mun yi imanin cewa an kusa warware rikicin domin an riga an dauki matakai masu muhimmanci na tattaunawa.” Matsayinmu ne, Mozambique ba ta goyon bayan kuwace kasa, ba za mu taba cewa yaki abu ne mai kyau ba, babu wanda ya isa ya kashe wani.”ya nanata.

Sabanin kasar Portugal, Mozambique na daya daga cikin kasashe 35 da suka ki kada kuri’a kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya da ke neman Rasha ta dakatar da mamaye  Ukraine, da kuma janye dakarunta. Duk da tattaunawar Ukraine da Rasha har yanzu ba a cimma tsagaita bude wuta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *