Da duminsa: Hukumar EFCC ta yi awon gaba da  da tsohon gwamna

Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati EFCC, sun yi awon gaba da sohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano.

An kama tsohon gwamnan ne a filin jirgin sama na Legas, sa’o’i kadan bayan mika mulkin jihar ga sabon gwamna Chukwuma Charles Soludo.

Ana kyautata zaton tsohon gwamnan yana kan hanyarsa  ne ta arcewa daga Najeriya zuwa Amurka lokacin da hukumar ta EFCC ta kama shi.

Jami’an hukumar, za su kai Obiano a ofishinsu.

kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, an kama tsohon gwamna Obiano ne, da misalin karfe 8:30 na dare. Dama dai tuni sunansa yana cikin jerin sunayen da ke hannun hukumar ta EFCC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *