Muhawara na ta kare ba don har yanzu ana musayar bayanai kan rahoton da dan majalisa Gudaji Kazaure ya fitar cewa a na karkatar da biliyoyin dala da babban banki ya tara daga kudaden da bankuan ke caji daga shigarwa ko cire kudi.
Kazaure ya ce kudin a Naira sun kai Naira tirilyan 89.9 da a kan tura su ga masu zuba jari ta zamba cikin aminci alhali kudin na gwamnati ne.
Kazaure wanda ya ce duk kokarin da ya yin a ganawa da shugaba Buhari da ya ce ya nada shi sakataren kwamitin bincike ya ci tura, amma gwamnan babban banki da su ke zargi na zaman beli ne.
Mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya fitar da sanarwa da ke cewa ministan shrari’a Abubakar Malami ne ke gudanar da aikin kwamitin a halin yanzu bayan rushe wanda Kazaure ke magana.
Shehu ya kara da cewa shugaba Buhari na kaunar aikin kwamitin da Malami ke jagorantar kuma kwamitin na gudanar da aikin sa don dawo da kudaden cajin zuwa asusun tara kudaden na bai daya.
Kazaure ya kalubalanci Garba Shehu da cewa tamkar ya na baiyana ra’ayin sa ne don bai ma san lokacin da a ka kafa kwamitin ba.