A takaice
Rasha ta tsare mutane sama da 250 saboda zanga-zangar nuna adawa da “ayyukan soji” da kasar ta ke yi a Ukraine, yayin da ake ci gaba da gwabza fada a mako na uku.
A Moscow babban birnin kasar an kama mutane da dama a dandalin Manezhnaya, kusa da fadar Kremlin. ‘Yan sanda sun tsare mutane a Saint-Petersburg a wajen zanga-zangar nuna adawa da matakin sojan Rasha a Ukraine.