Wani shiri da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi na kawo karshen matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan, yana ci gaba da gudana, kuma ana sa ran ganin cewa, karancin mai irin wannan bai sake dawowa a kasar ba.
Wani jami’in fadar shugaban kasar wanda ya bayyana hakan a karshen mako ya kara da cewa, dogayen layukan da aka yi fama dasu cikin ‘yan kwanaki kusan kowace jiha a kasar nan, zai kawo karshe ba tare da dogayen layuka ba.
Shirin wanda aka gabatar wa Majalisar Zartarwa ta Tarayya, a makon da ya gabata, Shugaba Buhari ya rattaba hannu ne a baya kafin ya bar kasar a makon da ya gabata a ranar Lahadin da ta wuce tare da bayyanannun muradun da suka hada da cimma matsaya kan musabbabin wannan karanci mai tare da aiwatar da sakamakon da ya samar.
A cewar majiyar, “an tsara shirin ne don yin duk abin da ya dace don kawo karshen matsalar karncin man cikin gaggawa tare da dakile wadanda ke da alhakin hakan a matakin farko don guje wa maimaituwar wannan.”
Majiyar ta bayyana cewa, abu mafi muhimmanci ga gwamnati shi ne, “wannan karancin mai ya zo karshe, kuma a kauce wa sake aukuwar hakan nan gaba.”