Buhari ya gargadi shugabannin jam’iyyar APC yayin da kan jam’iyyar ya rabu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi shugabannin jam’iyyar APC da su guji yin kaurin suna da kuma tada kayar baya.

Gabanin babban taron da za a yi a ranar 26 ga Maris, jam’iyya mai mulki a Najeriya ta rabu gida biyu inda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Buni ya dage cewa shi ne shugabanta na kasa.

Yanzu haka dai takwaransa na jihar Nijar, Sani Bello ne ke jagorantar jam’iyyar APC, lamarin da ya raba kan gwamnonin jam’iyyar da ‘yan majalisa da sauran mukarraban jam’iyyar.

Buhari ya shaida wa jiga-jigan jam’iyyar APC da su tsaya tsayin daka, tare da tabbatar da hadin kai muddin  jam’iyyar za ta ci gaba da samun nasara da kuma samun madafun iko a fadin kasar nan.

Shugaban a ta bakin mai magana da yawunsa Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya gaya wa mambobin “da su dubi kakkarfar jam’iyyar PDP  a baya, a yanzu ta lalace kuma ta yi tafiya irin haka, kuma ta koyi darasi na rashin haɗin kai, rashin adalci da rashawa.”

Sanarwar t ace,”Sun gaza a cikin shekaru sha shida suna mulki kuma sun gaza a matsayin ‘yan adawa.”

Shugaban y ace, “Yayin da kasar nan ke shirin tunkarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023, dukkanmu muna sa ran za a yi muhawara mai karfi a kan batutuwan da suka shafi al’amura da kuma abin da ke faruwa a jam’iyyar APC. Ya kamata ya zama abin koyi, ba wai sabani da muke gani ba.”

Buhari ya yi gargadin kada a kara daukar hankali gabanin babban taron na zaben sabbin shugabanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *