Gwamnan Ribas ya bukaci a ladabtar da mataimakin gwamna

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar PDP da su dauki matakin ladabtarwa a kan mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shu’aibu kan kalaman da ya yi ma jam’iyyar.

Gwamnan ya ce, ya rubutawa shugaban jam’iyyar ta PDP na kasa wasika yana neman a kafa kwamitin ladabtarwa kan mataimakin gwamnan.

Gwamna Wike ya bayyana wannan bukata ne a wajen kaddamar da titin Eastern Bypass a Fatakwal a ranar Asabar. Ya zargi Shu’aibu da yin barazanar cewa, akwai wata mafitar.

Ya ce “Wannan shi ne abin da nake magana game da rashin hukunta shi. Ina kallo ne a lokacin da wani Mataimakin Gwamna ke ta yawo a kafafen yada labarai, yana yi wa jam’iyyar barazana cewa, akwai wata mafitar da ta wuce PDP.”

“Wannan shi ne Mataimakin Gwamnan da ya durkusa ya roke mu a ba su laima. A yau, yana da hatsaniya don yiwa PDP barazana,” Inji Wike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *