An kwaso ’yan Najeriya 123 daga Ukrain

 

Kimanin ‘Yan Najeriya dari da ashirin da ukku da Gwamnatin Tarayya ta kwashe daga kasar Ukraine sun isa Abuja.

An taso da mutanen ne daga kasar Poland a cikin jirgin Air Peace da ya sauka a filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar 11 ga wannan wata na Maris da misalign karfe 1:20 na dare.

Tawagar gwamnatin tarayya,da sauran hukumomin da ke karkashin ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma (NEMA)ne suka tarbe su. Haka kuma akwai wakilan Ma’aikatar Harkokin Waje ta Tarayya da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa da kuma Hukumar Kula da Lafiya ta gami da Cibiyar yaki da Cututtuka ta Najeriya da dai sauransu.

Da yake jawabi a madadinsu Darakta Janar na hukumar NEMA Mustapha Habib Ahmed, Daraktan Binciken…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *