Jam’iyyar APC ta tabbatar da ranar 26 ga wannan wata a matsayin ranar babban taronta na kasa

Jam’iyyar APC, ta sake tabbatar da cewa ranar babban taronta na kasa a ranar 26 ga Maris, Da yake karin haske ga manema labarai kan ci gaban da aka samu kawo yanzu gabanin babban taron, wakilan matasa a kwamitin riko, Mista Ismaeel Ahmed, ya ce, kananan kwamitoci sun fara aiki.

Mista Ahmed wanda ke jagorantar kwamitin yada labarai na taron ya ce, ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da nasarar aikin.

Ya bayyana cewa, sun kuma jajirce wajen kare wa’adin gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, bayan da wata babbar kotun tarayya ta kore shi saboda ya koma APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *