Mun zabi Raila Odinga a matsayin dan takara a Zaben shugaban kasa na wannan shekara-Kenyatta

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya amince da tsohon abokin hamayyarsa Raila Odinga, a matsayin dan takara a babban zaben kasar, kamar yadda ya shaida wa taron jama’a da ke murna a Nairobi.

Wannan matakin na zuwa ne makonni 2 bayan da jam’iyyunsu suka hada karfi da karfe, a gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a watan Agustan wannan shekara, a karkashin tutar jam’iyyar Mr Kenyatta, Jubilee Party da kuma ta Odigan mai suna Orange Democratic Movement, hada ka da sauran kungiyoyin siyasa.

Wannan amincewa a hukumance ya haɗu da manyan jam’iyyun siyasa biyu na Kenya, waɗanda suka yi adawa da juna a lokutan zaɓe da dama.

A shekara ta 2018, Kenyatta da Odinga sun ba wa ‘yan kasar mamaki a lokacin da suka yi musabaha tare da ayyana sulhu da juna, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekarar 2017, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Raila Odiga, mai shekaru 77, gogaggen dan siyasa ne. Ya taba zama firaministan kasar Kenya tsakanin shekarar 2008 zuwa 2013.

Kokarin neman shugabancin Odinga na shekarar 2022 ya zo ne bayan dan siyasar ya sha kaye sau hudu a zaben shugaban kasa a shekarun 1997, 2007, 2013 da 2017.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan da aka kori tsohon magajin Kenyatta, William Ruto wanda kuma ke neman shugabancin kasar daga jam’iyyar Jubilee Paty.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *