Shugaban mulkin soja a Burkina Faso ya saka hannu  kan yarjejeniyar mika mulki

A ranar Talata ne, shugaban mulkin sojan kasar Burkina Faso, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ta tanadi wa’adin mika mulki na shekaru uku kafin a gudanar da zabe a kasar, kamar yadda wani wakilin kamfanin dillancin labarai na  AFP ya ruwaito.

“An tsaida wa’adin mika mulki ne watanni 36 daga ranar rantsar da shugaban kasa,” a cewar yarjejeniyar mika mulki da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda ya maye gurbin tsohon shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore a karshen watan Janairu.

Wa’adin mika mulki ya zarce na watanni 30 da kwamitin fasaha da gwamnatin mulkin soji ta kafa a farkon watan da ya gabata a wani daftarin doka da aka tattauna na tsawon sa’o’i da dama a tarurrukan gwamnatin da kungiyoyin fararen hula, a ranakun Litinin da Talata.

Tattaunawar ta hada da jam’iyyun siyasa, kungiyoyin kwadago, matasa da mata, da kuma mutanen da hare-haren ‘yan da’awar jihadi suka raba da muhallansu a Burkina Faso tun daga shekarar 2015.

Yarjejeniyar ta kuma tanadi cewa shugaban rikon kwarya “bai cancanci zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da na kananan hukumomi ba da za a shirya domin kawo karshen mika mulki.”

Wannan tanadi ya kuma shafi mambobi 25 na gwamnatin rikon kwarya.

Yarjejeniyar ta ayyana cewa, daya daga cikin manyan manufofin mika mulki shi ne “yakar ta’addanci, da maido da martabar yankin kasa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *