Ngige ya gana da shugaba Buhari kan yajin aikin malaman jami’a

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, domin su tattauna kan tattaunawar da gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i suka yi.

kungiyar ta fara yajin aikin ne, a ranar 14 ga watan Fabrairu domin matsa wa gwamnati lamba kan biyan wasu makudan kudade har naira tiriliyan 1.2.

Malaman sun kuma bukaci a amince da tsarin biyan kudi na  UTAS.

Ngige ya shaida wa manema labarai na fadar gwamnati cewa, an biya Naira biliyan 92 a matsayin alawus-alawus da kuma kudaden farfado da malama.

Da yake tunawa da yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar a watan Disambar 2020, Ministan ya ce, gwamnati ta cika Naira biliyan 40 na kudaden alawus-alawus na Ilimi ‘Earned Academic Allowance’ ga kungiyar malaman da sauran kungiyoyin.

“An kuma kashe naira biliyan 30 domin farfado da ita wanda kuma aka biya a karshen shekarar da ta gabata.

“An amince a biya Naira biliyan 22.127 daga karin kasafin kudin a matsayin alawus-alawus na shekarar 2021. An kuma biya wadannan kudaden a bara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *