Zaben 2023: Tinubu ne zabinmu duk da halin rashin lafiyarsa

Tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Abdulmumin Jibrin ya caccaki masu sukar jagoran jam’iyya mai mulki APC, Bola Ahmad Tinubu kan wani faifan bidiyo da ke nuna yadda hannunsa ke kyarma.

Abdulmumini Jibrin wanda ya wakilci Mazabar Kiru da Bebeji ta Jihar Kano a Majalisar Tarayya da ta gabata ya ce, Tinubu shi ne zabinsu a takarar Shugaban kasa mai zuwa, duk da matsalolin rashin lafiya da ake zargin sa da su.

Ya kuma bukaci masu sukar Tinubu, da su hada hannu  da dan takarar shugaban kasar shi kadai.

Majiyar mu ta ruwaito cewa, tun lokacin da shugaban jam’iyyar APC ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar, wasu fayafan bidiyo da dama suka bayyana a shafukan sada zumunta da ke bayyana rashin lafiyar da ake zargin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *