Shugaba Buhari ya tafi Landan domin hutun jinya

Tare da rahoton Africanews

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Landan hutun jinya na tsawon makonni biyu bayan ziyarar da ya kai kasar Kenya, kamar yadda kakakinsa Femi Adesina ya bayyana haka a wata sanarwa a yau Talata.

Muhammadu Buhari, mai shekaru 79 a duniya, ya ziyarci Landan sau da dama saboda duba lafiyarsa, tun lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2015, amma ba a taba bayyana yanayin rashin lafiyarsa ba. Ziyarar jinya ta karshe a Landan, wacce kuma ta dauki tsawon makonni biyu, ita ce  ta watan Yulin shekarar da ta gabata.

A yawancin lokuta, wadannan tafiye-tafiye na haifar da cece-kuce a Najeriya, inda tsarin kiwon lafiyar kasar ya gaza, yayin da likitoci kasa da 42,000 ke aiki ga sama da mutane miliyan 210 da kuma asibitoci sun lalace.

Muhammadu Buhari ya bar Najeriya ranar Litinin zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya, inda zai halarci bikin cika shekaru 50 da kafa hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya a ranakun Alhamis da Juma’a, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Yanayin lafiyar tsohon Janar din dai ya kasance batun muhawara a yakin neman zaben da ya gabata a shekarar 2019, inda ‘yan adawa ke ikirarin cewa ba shi da koshin lafiya wajen gudanar da mulki. Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben.

A farkon 2017, ya shafe watanni uku a Landan don jinya, wanda majiyoyin hukuma ba a taba bayyana su ba. Da ya dawo, ya ce “bai taba yin rashin lafiya haka ba” a rayuwarsa kuma an yi masa karin jini da dama.

Shugaba Buhari zai kammala wa’adinsa na biyu, a ranar 29 ga watan Mayun 2023,  kuma ya bayyana cewa ba ya da niyyar tsayawa takara karo na uku. Har yanzu dai babu wani dan takara da ya fito da zai maye gurbinsa, amma tuni jam’iyyar APC mai mulki ke da ‘yan takara da dama ciki har da fitaccen tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *