A zaben 2023 ne lokacin saka ma Bola Tinubu

Wata kungiyar siyasa dake fafutukar ganin an tsaida Bola Tinubu takarar shugabancin kasa a karkashin  jam’iyyar APC ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su mara masa baya.

Kungiyar ta ce tsohon gwamnan jihar Legas na cikin wadanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya a kasar nan, don haka ta bukaci ‘yan Najeriya da su nuna yakama ta hanyar mara masa baya a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Nasiru Daura, wanda ya yi jawabi a wajen taron kungiyar na kasa da aka gudanar a Abuja ya ce, “Tinubu mutum ne da ya yi fafutuka kuma ya yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya a daidai lokacin da wasu ke shiryagangamin mutum miliyan daya domin tallafa ma mulkin sojoji. A yau muna cin moriyar ‘yancin da ke tattare da dimokuradiyya.”

“Saboda haka Asiwaju, ya cancanci a saka masa ta hanyar goya masa  baya da katunan zabenmu, tare da  yi masa addu’a domin ya zama shugaban kasa.”

Darakta-Janar na Tinubu na kungiyar, Dokta Benjamin Johnny, ya bayyana Tinubu a matsayin cikakken dan dimokuradiyya wanda ya hada karfi da karfe da sauran ‘yan Najeriya masu neman ci gaba wajen kawo ribar dimokuradiyya a halin yanzu.

Tinubu ya yi ma Nijeriya da ‘yan Nijeriya abubuwa da dama ba tare da la’akari da kabila ko addini ba,’’ inji shi.

 “Shugabancin da ake yanzu, a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana aza harsashin kafa sabuwar Najeriya mai ayyuka daban-daban na samar da ababen more rayuwa da ci gaban dan Adam.”

“Tinubu ya taka rawa sosai wajen samun nasarar zaben Buhari, kuma ya rika nuna goyon bayansa ga gwamnati. Saboda haka, shi ne mafi cancantar ci gaba da gadonsa, ” in ji shi.

One thought on “A zaben 2023 ne lokacin saka ma Bola Tinubu

  1. Something else is that while looking for a good internet electronics shop, look for web shops that are regularly updated, trying to keep up-to-date with the hottest products, the very best deals, as well as helpful information on products and services. This will ensure that you are dealing with a shop that stays on top of the competition and provide you what you need to make educated, well-informed electronics buys. Thanks for the crucial tips I’ve learned from the blog.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *