Za a sake ba al’ummar Jihar Katsina damar yin Rijistar Gaggawa ta samun talafin annobar Korona wato RRR ga mutanen da ba su samu damar yi ba tun da farko da za ta fara ranar litanin, bakwai ga watan Maris mai kamawa.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Ofishin Kula da Rijistar Mutane Marasa Ƙarfi na Jihar Katsina wato SOCU, Marwana Abubakar Darma, a madadin Babban Jami’in shirin a Jihar Katsina, Aliyu Isa Girka.
Sanarwa ta bayyana cewa, mutanen da ke da sha’awar yin rijistar waɗanda kullen annobar cutar COVID-I9 ya shafi kasuwancinsu kuma ba su samu damar yin rijistar ba tun a karon farko, za su iya yin rijistar yanzu.
Sanarwa ta kuma buƙaci jama’a da su guje wa yin rijista sau biyu wanda hakan ya faru a lokacin gudanar da rijistar kashi na biyu kuma ya jaza masu rasa samun damar shiga cikin shirin waɗanda za su amfana da biyan tallafin nan gaba.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, wannan rijista da za a sake gudanar da ita nan ba da jimawa ba, za ta gudana ne tsawon sati ɗaya kachal, watau daga ranar Litinin, 7 zuwa 13 ga watan Maris idan Allah Ya kai mu.
Ta kuma buƙaci mazauna garuruwan Jihar Katsina da aka gudanar da shirin a baya, musamman ga waɗanda ba su samu yin rijista ba, da kada su bari a bar su baya.
Sanarwar ta kara da cewa, wannan rijista da za a sake buɗewa, dama ce ga ƙananan hukumomin da ba su samu ikon yi ba a baya sabili da dakatar da hanyoyin sadarwa ta wayoyin salula da aka yi yankunansu, sakamakon matsalar tsaro da aka fuskanta.
1. GRM officer Grievance Redress
Manager. 09077608755
2. Information Officer, 09079083723