Rundunar ‘Yan sandan Abuja ta ceto mutane 11 daga hannun ‘yan ta’adda

Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce, ta gano wani matsugunin masu garkuwa da mutane a wani dajin da ke unguwar Kuje a Abuja.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Josephine Adeh ya fitar ta ce, jami’an rundunar sun ceto akalla mutane goma sha daya da aka yi garkuwa da su a unguwar Gwargwada, yankin Kuje na yankin a ranar 17 ga Fabrairu wannan shekara.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa, harin wanda ya faru a ranar Asabar din da ta gabata, ya biyo bayan martanin gaugawa da rundunar ta bayar akan wani rahoto da ke cewa, wasu miyagu marasa gaskiya sun shiga dajin.

ya ce, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Babaji Sunday, ya umurci jami’an da su kewaye dajin domin kamo ‘yan ta’addan da kuma ceto sauran wadanda abin ya shafa.

A cewarsa, wadanda aka ceto tuni sun fara samun kulawar likitocin da suka dace kuma za su sake haduwa da iyalansu da zarar an tabbatar da lafiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *