Wata Makarantar al’umma mai suna “Gafai Community Secondary School, a ranar Litinin da ta mika shugabancin makarantar na kwana daya ga wasu zakarun dalibanta da suka zamo fitattau a fagen darussan da makarantar ke koyarwa.
Makarantar , ta mika shugabancin gudaran da makarantar ga daliban, ta yadda suka gabatar da duk ayyukan makarantar a tsawon yini kamar yadda shugabannin makarantar ke aiwatarwa.
A yayin tattaunawa da majiyarmu, shugabannin makarantar na Gafai Community Secondary School, sun bayyana dalilin yi ma wadannan daliban wannan karramawa a matsayin tagomashi a gare su saboda kwazon da suka nuna.
Muttaka Abdullahi, shugaban bangaren karamar makarantar (junior) ya bayyana cewa, “Dalilin da ya sa yin wannan shi ne domin kara jawo hankalin yara su kara maida hankali, su kara kwazo ga karatunsu.”
Shi ma Naziru Sani Shugaban bangaren babbar makarantar ya ce ,”Mun yi hakan ne don daliban su kara himmatuwa ga karatusu, domin su zama cikakkun mutane masu inganci, a fannin ilimi, kuma domin sauran dalibai su yi koyi da su.”